Isa ga babban shafi
Najeriya

Matsalar garkuwa da mutane na karuwa a tsakanin Abuja da Kaduna

Rahotanni daga arewacin Najeriya, sun ce masu yin garkuwa da mutane sun sake tare hanyar Abuja zuwa Kaduna a yammacin jiya Laraba da misalin karfe 3.

Hanyar da ta tashi daga Kaduna zuwa Abuja.
Hanyar da ta tashi daga Kaduna zuwa Abuja. The Guardian Nigeria
Talla

Tashin hankalin da ya auku a gaf da kauyen Akilibu ya tilastawa matafiya dakatawa a gefen hanya cikin jiran samun taimakon jami’an tsaro.

Rahotannin sun ce jama’a na cikin zulumin ne, sai aka yi sa’a jerin gwanon motocin Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i suka tunkaro kan hanyar da nufin isa Abuja.

Ba tare da bata lokaci ba, jami’an tsaro madaka kare, dake tare da Gwamnan suka fatattaki ‘yan bindigar, wadanda suka tsere cikin daji.

Karo na uku kenan da masu satar mutane ke cin Karensu ba babbaka a kan hanyar ta Abuja zuwa Kaduna, inda a ranar Litinin suka sace mutane akalla 30, koda yake jami’an yan sabda sun musanta rahoton.

Kwana guda kuma bayan faruwar tashin hankalin, masu satar mutanen suka sake yin awon gaba da wasu matafiya kimanin takwas a dai kan hanyar ta Kaduna zuwa Abuja kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Mutane da dama, na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan matsalar satar mutane da yi garkuwa da su, da ke dada girmama a sassan Najeriya, musamman arewacin Najeriya, inda suka bukaci gwamnati ta ayyana dokar ta baci kan matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.