Nafisa Abdullahi ta soki Buhari kan kisan Zamfara
Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood na Hausa, Nafisa Abdullahi ta caccaki shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari saboda yadda ya yi gum da bakinsa game da kashe-kashen da ake yi wa al’umma a wasu kauyuka da ke jihar Zamfara.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Jarumar ta soki shugaban ne biyo bayan sakon ta’aziya da ya aika ta shafin Twitter ga iyalan wani matashi, Johnson Kolade da jami’an ‘yan sanda suka kashe shi a birnin Lagos.
A martanin da ta mayar wa Buhari, Nafisa ta ce, “ ka yi magana game da daruruwa da dubban mutanen da ake kashewa a Zamfara da sauran sassan arewacin kasar kafin kisan da aka yi wa Kolade, ko kuma ka magance matsalar a lokaci guda."
Jarumar ta kara da cewa, shugaban na tsoron tsokokaci kan kashe-kashen da ake yi a arewa, amma ya yi magana game da kisan da ya faru a kudancin kasar a cewarta.
A sakon da ya aika, shugaba Buhari ya bai wa 'yan Najeriya tabbacin cewa, za a hukunta jami'an 'yan sanda biyu da suka harbe Kolade har lahira a jihar Lagos, yana mai nuna takaicinsa kan al'amarin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu