Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnati za ta yi amfani da tsafi kan maharan Zamfara

Sakamakon yadda hare-haren 'yan bindiga na jihar Zamfara a Najeriya ke ci gaba da ta’azzara, gwamnatin jihar ta dauki matakin daukar masana Kauda-Asiri dubu 1 da 700 domin taimaka wa jamian tsaro samun bayannai domin magance yawan kai hare-haren 'yan bindigar. Gwamnatin jihar ce ta sanar da hakan a taron majalisar tsaro da ta gudanar da sarakunan gargajiya na jihar. Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa don sauraren cikakken rahoton daga bakin wakilinmu, Faruk Muhammad Yabo.

Gwamnati za ta yi amfani da masana sihiri wajen yaki da masu kashe mutane a Zamfara
Gwamnati za ta yi amfani da masana sihiri wajen yaki da masu kashe mutane a Zamfara RFI/Hausa
Talla
02:59

Gwamnati za ta yi amfani da asiri kan maharan Zamfara

A bangare guda, gwamnatin jihar ta ce, 'yan bindigar sun hallaka akalla 'yan banga da wasu mutane 50 sakamakon arangmar da suka yi da su a karamar hukumar Kauran-Namoda.

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Sanusi Rikiji ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci karamar hukumar domin jajanta wa masarautar karamar hukumar kan abinda ya faru.

Rikiji ya ce, bayanan da suka samu sun nuna musu cewar, 'yan bangar sun hada kansu ne a garin Sakajiki da ke karamar hukumar Kauran-Namoda domin fuskantar 'yan bindigar a daji, lokacin da lamarin ya faru.

Shugaban Majalisar Dokokin ya bayyaan rashin kwarewar 'yan bangar da kuma makaman da 'yan bindigar ke da su a matsayin abinda ya bada galaba akan su.

Daga nan sai ya bayyana cewar, Gwamnan Jihar Abdulaziz Yari ya bukaci Sarakuna da su janyo hankalin 'yan bangar da su tsaya kan taimaka wa jami’an tsaro a maimakon fuskantar 'yan bindigar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.