rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rahotanni Najeriya Katsina Zamfara Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan Najeriya sun soma rububin sayen maganin bindiga

media
Misalin yadda wani mutum ke hada maganin kau da bara ga jami'an vigilante da ke fada da mayakan Boko Haram a garin Maiduguri. REUTERS/Joe Penney

A Nigeria zaman fargaba da rashin madafa, ya tilastawa wasu al'ummomi dake fama da matsalar masu satar jama'a, amfani da wani tsimi a matsayin maganin bindiga da kuma garkuwar harshashi a jihar Katsina.

Garkuwa da jama'a dai na kara kazancewa a wannan jiha, kamar yadda matsalar ta yi kamari a Zamfara, inda a baya-bayan nan akai awon gaba da magajin garin Daura, kani ga Sarkin Daura kuma Surukin dogarin Shugaba Buhari watau Alh. Musa Umar.

Daga Bauchi ga rahoton Shehu Saulawa da ya ziyarci jihar ta Katsina.


Rahoto kan yadda 'yan Najeriya suka soma rububin sayen maganin bindiga 02/05/2019 - Daga Shehu Saulawa Saurare