Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya tsawaita wa'adin gwamnan bankin Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tsawaita wa’adin Shugaban Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emiefele, inda zai kara wasu shekaru 5 nan gaba, matakin da haifar da banbancin ra'ayoyi a kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da shugaban babban bankin kasar, Godwin Emefiele
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da shugaban babban bankin kasar, Godwin Emefiele Daily Trsut
Talla

Tuni shugaba Buhari ya bukaci Majalisar Dattawan Kasar da ta tabbatar da Emefile a matsayin wanda zai ci gaba da jagorancin babban bankin.

Sai dai wannan al’amari ya haifar da cece-kuce a sassan kasar, inda wasu masa tattalin arzikin ke cewa, bai dace a tsawaita wa’adinsa ba, yayinda wasu ke ganin cewa, ya taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tattalin arzikin kasar.

Masana irinsu Farfesa, Uche Uwaleke na jami’ar jihar Nasarawa ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa, Emefiele ya taka rawar gani kuma ya tafiyar da aikinsa bisa doran muradun gwamnatin shugaba Buhari.

A yayin zantawarsa da sashen Hausa na RFI, Dr. Kasimu Kurfi, masannin tattalin arziki ya ce, Emefiele bai cancanci a tsawaita masa wa’adinsa ba saboda gazawarsa wajen gudanar da ayyukan bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

A cewar Kurfi, shugabannin CBN da suka gabace shi, sun fi shi tabuka abin kirki domin kuwa an ga ayyukan da suka yi a zamaninsu.

"Gwamnan ma ba tattalin arziki ya karatant ba" in ji Kurfi.

00:49

Ra'ayin Kasimu Kurfi kan kara wa Emefiele sabon wa'adin shugaban CBN

Emefiele zai kasance mutun na farko da ya samu karin wa’adin shekaru biyar a kujerar shugaban CBN tun shekarar 1999, lokacin da Najeriya ta koma mulkin demokradiya.

Tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan ne ya nada shi akan kujerar shugaban babban bankin domin maye gurbin Sanusi Lamido Sanusi, Sarkin Kano na yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.