Isa ga babban shafi
Najeriya

Dattawan Kano sun gargadi Buhari da Ganduje kan sabbin masarautu

Wasu dattawan Jihar Kano sun yi gargadin cewa matakin da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya dauka, na nada sabbin Sarakuna guda 4 masu daraja ta 1, ka iya haifar da rikici.

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, yayin taya shugaban Najeriya Muhammadu Buhari murnar lashe zaben shugaban kasa.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, yayin taya shugaban Najeriya Muhammadu Buhari murnar lashe zaben shugaban kasa. Kano State Government
Talla

Wasu daga cikin Dattawan da suka sa hannu kan sanarwar gargadin da suka fitar, sun hada da Dakta Abubakar Sadiq Muhammad, Bashir Yusuf Ibrahim, Bashir Tofa, Dakta Usman Bugaje, da kuma Farfesa Jibril Ibrahim, wadanda suka ce kirkirar karin masarautun 4, zai siyasantar da tsarin mulkin gargajiya, lamarin da zai haifar da rabuwar kawunan jama’a da kuma rikici a nan gaba.

Sanarwar ta kuma bukaci shugaban Najeriya Muhammdu Buhari ya sa baki cikin maganar, domin tsawatarwa Ganduje ya janye matakin da ya dauka, zalika ya kamata gwamnatin Najeriya ta baiwa wannan sabuwar matsala da ta kunno kai muhimmancin da ya kamata.

Jan hankalin Dattawan na Kano, ya zo ne bayan da Babbar kotun Jihar ta soke nadin sabbin sarakunan da Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi, inda ta ayyana matakin a matsayin wanda ya saba wa doka, yayinda ta bukaci a koma kan tsarin da ake kai kafin ta kammala sauraren karar da aka shigar a gabanta.

Masu Zaben Sarki a masarautar Kano da suka hada da Sarkin Dawaki Maituta Alhaji Bello Abubakar da Sarkin Bai, Alhaji Mukhtar Adnan, da Madakin Kano, Alhaji Yusuf Nabahani, da Makaman Kano, Alhaji Sarki Ibrahim Makama ne suka garzaya kotun don kalubalantar matakin Ganduje na kirkirar sabbin masarautu hudu.

Masarautun da gwamnan Kano Ganduje ya daga zuwa masu daraja 1 sun hada da Rano, Karaye, Bichi da kuma Gaya.

Hakan na nufin jihar Kano ta rabu zuwa masarautu 5, inda a yanzu kananan hukumomi 8 ne kawai suke karkashin mulkin Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II, yayinda aka raba sauran kananan hukumomi 36 zuwa karkashin sabbin Sakaruna masu daraja ta 1 da aka nada.

A halin yanzu masarautar Bichi na da kananan hukumomi 9 da ke karkashinta, da suka hada da Bagwai, Shanono, Kunchi, Tsanyawa, Bichi, Dambatta, Dawakin Tofa, Tofa da kuma Makoda.

Masarautar Gaya ma dai kananan hukumomi 9 ke karkashinta, da suka hada da Ajingi, Albasu, Gaya, Wudil, Garko, Dawakinkudu, Gabasawa, Gezawa da kuma Warawa.

Masarautar Karaye ta kunshi kananan hukumomin, Garunmalam, Kabo, Rimingado, Madobi, Gwarzo, Karaye, da kuma Rogo.

A karshe masarautar Rano a halin yanzu na da kananan hukumomi 10 da suka kunshi, Kibiya, Takai, Sumaila, Kura, Doguwa, Rano, Bunkure, Tudunwada, Kiru da kuma Bebeji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.