Majalisar Najeriya ta amince a sauya ranar Dimokradiya a kasar
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da dokar ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar Dimokiradiya da kuma hutu a fadin kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Amincewa da dokar na zuwa kusan shekara guda da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sanar cewa, za a sauya ranar Dimokradiya ta kasar daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni.
Tuni Majalisar Wakilai ta amince da matakin a nata bangaren.
Kodayake wasu su daga cikin mambobin Majalisar Tarayyar Najeriya sun soki wannan matakin na shugaban kasa, yayinda wasu suka yi madalla da shi.
Yanzu haka za a mika doka ga shugaba Buhari domin rattaba hannu akai.
An sauya ranar Dimokradiyar ce domin karrama marigayi Moshood Abiola da ake kallo a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa da aka gudanar a shekarar 1993.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu