rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Zaben Najeriya PDP APC Muhammadu Buhari

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan siyasar da suka fadi zabe ke haddasa matsalolin tsaro'

media
Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed. REUTERS/Afolabi Sotunde

Gwamnatin Najeriya ta bakin ministan yada labaranta Lai Mohammed, ta ce tana da kwararan shaidun cewa jam’iyyar adawa ta PDP na shirin yi wa shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa da salon tayar da rikici a kasar, ta yadda mulkinta zai gagara.


Wannan zargi dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da babban hafsan hafsoshin sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya bayyana cewa wasu ‘yan siyasa da suka sha kaye a zabukan da suka gabata ne ke shirya makarkashiyar ta’azzarar matsalar tsaro a wasu sassar kasar.

Magaji Bala Matazu, jagora ne na jam’iyyar APC a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, a Najeriya, yayin tsokaci kan zargin ya ce tabbas biri yayi kama da mutum, la’akari da yadda kokarin gwamnati mai ci na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar ‘yan kasar ke fuskantar matsala ta tufka da warwara.

Magaji Bala Matazu jagoran jam’iyyar APC a karamar hukumar Chikun da ke Kaduna 20/05/2019 - Daga Michael Kuduson Saurare

Sai dai a nashi bangaren ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed, fitowa yayi fili yana bayyana jam’iyyar adawa ta PDP a matsayin wadda ke jagorantar haddasa karuwar matsalolin tsaro a sassan kasar, zargin da bai yi wa ‘yayan jam’iyyar dadi ba, kamar yadda Mohamed Hamisu Dantajiri, shugaba na jam’iyyar PDP a karamar hukumar Kaduna ta Arewa a ya maida martani, inda ya ce borin kunya gwamnatin APC ke yi domin kuwa sun gaza cika alkawuran da suka yiwa talakawan Najeriya, kuma lokaci zai nuna mai gaskiya da maras ita.

Mohamed Hamisu Dantajiri shugaban jam’iyyar PDP a karamar hukumar Kaduna ta Arewa 20/05/2019 - Daga Michael Kuduson Saurare

Yanzu dai kallo ya koma sama, saboda al’ummar Najeriya musamman ma wadanda matsalar tsaro ke ci wa tuwo a kwarya, sun zuba idanu hadi da sauraron lokacin da za a kawo karshen wannan ta’asa, da kuma zakulo masu hannu a cikinta.