Isa ga babban shafi
Najeriya - Kaduna

Yan sanda sun kama mai ikirarin karya kan masu satar mutane

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ta bayyana kame Alhaji Musa, mutumin da ya yi ikirarin karya na cewa masu garkuwa da mutane za su sace shi a unguwar Kawo, lamarin da ya kai ga jikkata wasu mutane da basu da laifin komai.

Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya.
Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya. AFP
Talla

A ranar Litinin da ta gabata, daruruwan mutane suka datse wani sashi na manyan hanyoyin Kaduna zuwa Abuja, da kuma Kaduna zuwa Zaria, don nuna bacin rai kan yadda wani mutum ya rasa ransa, wasu kuma suka jikkata, bayan da harsashin da jami’an ‘yan sanda suka harba ya same shi bisa kuskure.

Rahotanni sun ce lamarin ya samo asali ne bayan da mazauna unguwar Kawo a Kaduna suka samu labarin cewa wasu masu garkuwa da mutane uku na kokarin sace wasu mazauna yankin.

Jin labarin ya sa jama’a datse hanyoyin shiga unguwar, zalika su ka kurewa masu garkuwa da mutanen gudu har suka yi nasarar kama guda tare da kone shi nan take,tare da jikkata wani guda, saura guda biyu kuma suka tsere.

Sai dai a lokacin da rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ke Karin bayani kan al’amarin, ta ce mutanen da suka je unguwar Kawodomin tafiya da Alhaji Musa, jami’an ’yan sanda ne daga Legas, la’akari da cewa akwai zargin da ake masa na aikata almundahana.

Domin gujewa doka ne kuma mutumin yayi ikrarin cewa za a sace shi, hakan ya jawo hankalin jama’ar da ke kusa, abinda yasa suka fusata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.