rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Zamfara Katsina Sokoto

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

UNHCR:Yan Najeriya sama da 20,000 sun tsere zuwa Nijar

media
Wasu daga cikin 'yan gudun hijira da suka tserewa muhallansu a wasu kauyukan jihar Zamfara 10. RFIHAUSA

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace tashin hankalin da ake samu na Yan bindiga a Jihohin Sokoto da Zamfara da katsina dake Najeriya sun tilastawa mutane akalla 20,000 tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar domin samun mafaka daga watan Afrilu zuwa yanzu.


Kakakin hukumar Babar Baloch ya shaidawa manema labarai a Geneva cewar rikicin Yan bindigar bashi da nasaba da Boko Haram, sai dai mutanen na tserewa hare haren Yan bindiga ne saboda dalilai da dama da suka hada da rikici tsakanin makiyaya da manoma dake da nasaba da kabilanci da kuma masu garkuwa da mutane domin karbar kudi.

Baloch yace matsalar tafi kamari a Jihar Zamfara wadda ta haifar da rasa dimbin rayuka abinda ya sa gwamnatin Najeriya tura dakaru 1,000 bara zuwa Jihar.

Hukumar tace wannan na daga cikin dalilin da ya sa gwamnatin Najeriya ta haramta hakar zinare a Zamfara saboda zargin cewar masu aikin na taimakawa tashin hankalin da ake samu.