rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Zaben Najeriya Muhammadu Buhari APC PDP

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rashin jawabin Buhari ga 'yan Najeriya ya janyo ce-ce-ku-ce

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin rantsuwar kama aikin wa'adin shugabancinsa na biyu. REUTERS/Afolabi Sotunde

A ranar Laraba 29 ga watan Mayu na 2019, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, suka yi rantsuwar kama aikin shugabancin kasar wa’adi na biyu, a babban filin taro na Eagle Square da ke birnin Abuja.


Ana kammala bikin rantsuwar ne shugaban na Najeriya tare da mataimakinsa, da kuma sauran mukarrabai suka bar filin taron ba tare da gabatar da jawabi na musamman ga ‘yan Najeriya ba, kamar yadda wasu ke zato.

Rashin gabatar da jawabin ne kuma ya jawo ce-ce-ku-ce daga bangaren ‘yan adawa, inda jam’iyyar PDP ta soki shugaban kan yadda ya gaza yin amfani da damar bikin rantsuwar, wajen gabatar da jawabi ga ‘yan kasa, kan muhimman batutuwa.

A cewar PDP hakan na nufin cewa, shugaban ba shi da wani sabon shiri, ko kyakkyawar manufa da zai gabatar ga ‘yan Najeriya.

Su kuwa jam’iyyun SDP da ADC sun bayyana rashin gabatar da jawabin shugaban ne, a matsayin nunawa ‘yan Najeriya cewa basu cancanci a basu kimar yi musu karin bayani kan sabbin shirye-shiryen gwamnati ba.

Sai dai masu iya magana sun ce ‘kowa da kiwon da ya karbe shi….’ Domin yayinda wasu ke sukar shugaban na Najeriya kan rashin gabatar da jawabi yayin bikin rantsar da shi a karo na biyu, wasu cewa suke yi matakin yayi daidai, ‘wai mai ido daya ya leka shantu’ domin duk abinda ‘yan Najeriya ke bukatar ji daga bakin Buhari, ya yi karin bayani akai yayin zantawarsa da manema labarai da aka yada ta kafar talabijin din kasar NTA a ranar Talata, gabannin bikin rantsar da shi.

Yayin zantawarsa da menama labaran, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sha alwashin baiwa wadanda suke kiransa da sunan ‘baba go slow’ mamaki yayin wa’adin mulkinsa na biyu.

Yayinda yake shan alwashin baiwa ‘yan Najeriya mamaki a zangon shugabancinsa na 2, Buhari ya yi alkawarin tabbatar da cewa an yiwa rundunar ‘yan sandan kasar da kuma sashin shari’a garambawul.

Kan batun matsalolin tsaro kuwa, da suka hada da hare-haren ‘yan bindiga, barayin shanu, da kuma garkuwa da mutane, shugaban na Najeriya da yayi alkawarin kawo karshen matsalolin, ya dora kaso mafi tsoka na alhakin tabarbarewar tsaron akan jami’an ‘yan sanda da kuma shugabannin al’umma a unguwanni, da kuma kauyuka zuwa sama.

Kwana guda bayan kammala bikin rantsar da shi a zagon mulki wa’adi na biyu, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tattaki zuwa kasar Saudiya domin halartar taron kasashen Musulmi na kungiyar OIC, karo na 14 da zai gudana a birnin Makkah a karkashin jagorancin Sarki Salman bin Abdulaziz Al Sa’ud.