rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Kaduna

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kaduna: Jagororin addini sun yi tsokaci kan dokar tantance masu wa'azi

media
Harabar ginin zauren majalisar dokokin jihar Kaduna. PM News

Jagororin addini a Kaduna da ke Najeriya, sun bayyana matsayinsu kan dokar tantance bada lasisin gabatar da wa’azi da majalisar dokokin jihar Kaduna ta amince da ita.


Yayinda yake tsokaci kan matakin, shugaban kungiyar mabiya addinin kirista CAN a jihar ta Kaduna, Joseph Hayab, wanda ya bukaci gwamnan jihar Nasir El Rufa’I ya jinkirta sawa dokar hannu, yace suna kan gudanar da nazari, kuma za su dauki matakin shari’a kan majalisar dokokin jihar idan basu gamsu da dokar ba.

Sai dai ana ta bangaren kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta hannun sakatarenta Yusuf Adamu, ta yi maraba da dokar.

A ranar Juma’ar da ta gabata Majalisar dokokin jihar Kaduna, ta amince da dokar sa ido kan malamai masu wa’azi daga bangaren Musulmi da Kirista, da tantance wadanda za ‘a baiwa lasisi a matsayin shaidar amincewar gwamnati.

Zalika a karkashin dokar, duk wanda aka samu da laifin kunna wa’azi, ko gabatar da shi, ta hanyar amfani da na’urar amsa kuwwa a masallaci ko mujami’a, daga misalin karfe 11 na dare zuwa 4 na safe, zai fuskanci hukuncin biyan tarar da ba za ta gaza naira dubu 200 ba, ko kuma daurin akalla shekaru 2 ko ma sama da haka.