rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Zaben Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rikici ya mamaye zaben 2019 a Najeriya- HRW

media
Human Right Watch ta ce, an samu koma-baya wajen magance rikicin zabe a 2019 idan aka kwatanta da zabukan shekarun baya The Guardian Nigeria

Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta Human Rights Watch ta yi zargin cewa, hare-hare da tashin hankali sun mamaye zaben shugaban kasar Najeriya da ya gudana a wannan shekara, yayinda ta zargi jami’an soji da 'yan sanda da hannu wajen haddasa matsalolin da aka samu.


Kungiyar ta ce, an samu hare-haren kungiyar Boko Haram da rikicin Fulani makiyaya da manoma da kuma karuwar hare-haren ‘yan bindiga har ma da garkuwa da jama’a a lokacin gudanar da zaben a wasu jihohin kasar.

Kazalika kungiyar ta bayyana cewa, ‘yan bindiga sun dirar wa wasu rumfunan zabe tare da kai farmaki kan masu kada kuri’u da ‘yan jarida da masu sanya ido a zaben musamman a jihohin Rivers da Kano.

Human Right Watch ta caccaki jami’an tsaro musamman ‘yan sanda kan yadda suka yi sakaci wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yayin zaben na 2019.