Isa ga babban shafi
Najeriya

Abubuwan da Buhari zai mayar da hankali a kai a wa'adi na biyu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jaddada aniyarsa ta bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma yaki da matsalar ta’addanci.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a lokacin da yake karbar rantsuwar kama aiki a wa'adinsa na biyu
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a lokacin da yake karbar rantsuwar kama aiki a wa'adinsa na biyu REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A yayin jawabin bikin ranar dimokiradiyar da aka gudanar a birnin Abuja wanda ya samu halartar daruruwan mutane cikinsu har da shugabannin kasashen Afrika da wakilan kasashen duniya, Buhari ya ce, ayyukan ta’addanci da matsalar tsaro sun zama ruwan dare, amma gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen shawo kan matsalar.

Shugaba Buhari ya bayyana yadda alkiblar gwamnatinsa ta yanzu za ta kasance da suka hada da zakulo shahararrun 'yan Najeriya da abokansu domin aiwatar da manufofin gwamnati.

Daga cikin manufofin har da inganta manyan makarantu da cibiyoyin bincike domin sanya Najeriya a sahun gaba wajen fasahar zamani da kuma kara zuba jari wajen harkar bada lafiya daga matakin farko zuwa na karshe da horar da ma’aikatan lafiyar da kuma samar da kayan aiki na zamani.

Dangane da noma da samar da abinci, shugaba Buhari ya ce, manoman Najeriya sun taka rawar gani wajen samar da shinkafa da masara da rogo da kaji da taki da kuma iri, saboda haka gwamnati za ta taimaka musu ta hanyoyi daban daban don ganin sun fitar da amfanin gonarsu zuwa kasashen duniya.

Buhari ya bayyana damuwa kan yadda ake sare itatuwa domin samun makamashi wanda ke yi wa dazukan kasar illa, inda yake cewa abin takaici ne kasar da ke fitar da ton miliyan 2 na iskar gas da ake girki da shi, bata iya amfani da rabin ton miliyan guda, abinda ya zama dole gwamnati ta dauki matakin gyara domin ganin jama’a sun rungumi iskar gas.

Shugaban kasar ya ce, yanzu haka gwamnati na gudanar da aikin gina hanyoyi da gadaje a sassa daban daban na kasar da suka kai kilomita 2,000, domin taimaka wa jama’a a harkar sufuri da kuma fitar da amfanin gonaki, yayinda a bangare daya kuma ake aikin gina layin dogo da tashoshin jiragen sama domin inganta harkar sufuri.

Buhari ya bayyana cewar, arzikin iskar gas da Najeriya ke da shi ya zarce na man fetur, yayinda kasar ta zama mai fitar da sinadarin yuriya da ake sarrafawa daga iskar gas, a daidai lokacin da gwamnati ke bukatar masu zuba jari domin inganta wannan bangaren.

A karshe shugaban kasar ya gargadi daidaikun mutane da kungiyoyin da ke yi wa jama’ar kasar barazana ko kuma masu sace dukiyar kasa domin azurta kansu tare da masu tinzira talakawa domin tada hankali, inda yake cewa lallai za su gamu da fushin hukuma.

Buhari ya ce gina kasa na daukan dogon lokaci, kuma a shirye suke su tabbatar da cewar Najeriya ta yi aiki yadda kowa zai ci moriyar ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.