Isa ga babban shafi
Najeriya

UNICEF ta koka kan amfani da yara a hare-haren kunar bakin wake

Asusun tallafawa ilimin kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF, yayi tur da yadda kungiyar Boko Haram ke amfani da kananan yara wajen kai hare-haren bam na kunar bakin wake a Najeriya.

Wasu kananan yara a garin Chibok na jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.
Wasu kananan yara a garin Chibok na jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya. tefan Heunisstefan/Getty Images
Talla

UNICEF ta bayyana hakane a ranar litinin, yayin da take raddi kan hare-haren kunar bakin waken da Boko Haram ta kai jama’a da ke gidan kallo a garin Konduga, inda mutane 30 suka halaka, wasu sama da 40 suka jikkata.

Mazauna garin da suka shaida faruwar lamarin sun ce wasu kanananyara uku ne suka kai harin kunar bakin waken na Konduga, 2 daga cikinsu mata da kuma namiji daya.

Hukumar ta majalisar dinkin duniya ta ce harin na Konduga ya sa adadin kananan yaran da kungiyar Boko Haram ta yi amfani da su wajen kai hare-haren kunar bakin wake kaiwa 5, daga farkon shekarar 2019 zuwa yanzu.

Wani rahoto da UNICEF ta fitar a shekarar 2018, yace kananan yara 48 Boko Haram ta yi amfani da su wajen kai hare-haren kunar bakin wake, daga cikinsu kuma yara mata 38 ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.