Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya na shirin haramta almajirci saboda tsaro

Gwamnatin Najeriya na duba yiwuwar haramta tsarin almajirci da zummar magance matsalar tsaro da ke addabar kasar kamar yadda mashawarcin shugaban kasa kan al’amuran tsaro, Babagana Monguno ya bayyana.

A can baya, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana takaicinsa kan yadda almajirai ke yawo da robobi suna neman abinci
A can baya, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana takaicinsa kan yadda almajirai ke yawo da robobi suna neman abinci PM News
Talla

Monguno ya bayyaana haka ne ga manema labarai jim kadan da kammala taron Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa da mataimakin shugaban kasar, Yemi Osibanjo ya jagoranta a fadar gwamnati da ke birnin Abuja a ranar Alhamis.

A cewar Monguno, “ yana da matukar muhimmanci a haramta wasu kungiyoyin da ke kai-kawo da sunan neman wani nau’in ilimi da ya yi hannun riga da tsarin gwamnati, sannan kuma su fara haifar da tarin matsaloli ga al’umma.”

Monguno ya yi karin bayani game da matakin , inda ya ke cewa, ba wai za a musguna wa almajiran ba ne ta kowanne yanayi, face aiki tare da gwamnatocin jihohin kasar don ganin an tilasta amfani da tsarin ilimi ga kowanne yaro.

Mashawarcin na shugaban kasa kan tsaron, ya bayyana cewa, suna son su yi amfani da makamancin tsarin da aka yi amfani da shi a kudancin Najeriya a tsakankanin shekarun 1950-60, lokacin da da Firimiyar yankin ya sanya ilimi kyauta kuma wajibi a matakan firamare da sakandare.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalolin ta’addancin kungiyar Boko Haram da barayin da ke satar jama’a domin karbar kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.