Isa ga babban shafi
Najeriya

"Gwamnatin Najeriya za ta jinkirta haramta almajiranci"

Kakakin shugaban Najeriya malam Garba Shehu, yace gwamnatin kasar ba za ta aiwatar da matakin da ta ce zata dauka na haramta almajiranci cikin gaggawa ba.

Gwamnatin Najeriya za ta jinkirta aiwatar da matakin haramta almajiranci a kasar.
Gwamnatin Najeriya za ta jinkirta aiwatar da matakin haramta almajiranci a kasar. The Economist
Talla

A ranar Alhamis da ta gabata, mai baiwa gwamnatin Najeriya shawara kan tsaro Manjo Janar Babagana Munguno mai ritaya, ya ce gwamnati na shirin haramta almajiranci, a wani bangare matakan magance matsalolin tsaron kasar da kuma bara.

Monguno ya bayyana haka ne ga manema labarai jim kadan da kammala taron Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa da mataimakin shugaban kasar, Yemi Osibanjo ya jagoranta a fadar gwamnati da ke birnin Abuja.

A cewar Monguno, “ yana da matukar muhimmanci a haramta wasu kungiyoyin da ke kai-kawo da sunan neman wani nau’in ilimi da ya yi hannun riga da tsarin gwamnati, sannan kuma su fara haifar da tarin matsaloli ga al’umma.”

Monguno ya yi karin bayani game da matakin, inda ya ke cewa, ba wai za a musguna wa almajiran ba ne ta kowanne yanayi, face aiki tare da gwamnatocin jihohin kasar don ganin an tilasta amfani da tsarin ilimi ga kowanne yaro.

Sai dai a ranar Juma’a gwamnatin Najeriyar, ta ce ba za’a aiwatar da matakin ba, har sai ta kammala ganawa da dukkanin wadanda abin ya shafa da sauran masu ruwa da tsaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.