rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Zamfara

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Zamfara: 'Yan bindiga sun gindaya sharuddan ajiye makamai

media
'Yan bindiga sun gindaya sharuddan ajiye makamai. Information Nigeria

'Yan bindiga a jihar Zamfara da ke Najeriya sun gindaya sharuddan da suka ce idan aka cika za su ajiye makamansu.


Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Zamfara Usman Nagoggo ne ya sanar da matsayar ‘yan bindgar, yayin ganawa da masu ruwa da tsaki a fannin tsaron jihar.

Cikin sharuddan da yan bindigar suka gindaya akwai daina kashe Fulanin da ake zargi a kasuwannin kauye da wasu jami’an tsaron sa kai ke yi a sassan jihar, zalika yan bindigar sun bukaci basu damar halartar kasuwanni ba tare da tsangwama ba.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce gindaya sharuddan da ‘yan bindigar suka yi, ya biyo bayan yunkurin ganin gwamnati ta bi matakin sulhuntawa da su.