rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari Ta'addanci BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Buhari na neman hadin kan duniya a yaki da manyan laifuka

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin taron kasa-da-kasa Reuters/AFOLABI SOTUNDE

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci hadin kan kasashen duniya wajen yaki da manyan laifuffukan da ake yi a kasashe daban daban.


Yayin kaddamar da wani rahotan taron tsaron da akayi a Munich dake kasar Jamus, Buhari ya bukaci tara kudade a matakin duniya domin yaki da masu aikata irin wadanan laifuffuka inda yake cewar babu wata kasa da zata iya yi ita kadai.

Shugaban ya bayyana rashin tsaron da ake samu a iyakokin kasashe da dama a matsayin abinda masu aikata laifuffuka ke amfani da shi wajen biyan bukatun kan su da suka hada da safarar kwayoyi da makaman da ake ayyukan ta’addanci da su.

Buhari yace cigaban fasaha wanda ya inganta hulda tsakanin mutanen kasashe da kuma samar da hanyoyin hulda da kasuwanci sun kuma haifar da matsalolin da suka shafi tsaro, ganin irin laifuffukan da ake aikatawa wadanda suka haifar da matsaloli a Yankin Afirka ta Yamma da suka hada da ayyukan ta’addanci da kuma safarar kwayoyi wadanda ke matukar illa ga jama’a.

Shugaban na Najeriya ya kuma ce Yankin Afirka ta Yamma na matukar fama da radadin safarar mutane da kwaya da kuma ayyukan ta’addanci, inda ya sha alwashin cigaba da yaki da cin hanci da matsalar tasro musamman akan iyakokin kasar.