rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Sokoto Katsina

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga a Sokoto da Katsina

media
Wasu dakarun sojin Najeriya. Pulse.ng

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana kame yan bindiga 25 da kuma halaka wasu da dama, yayin artabu da su a jihohin Katsina da Sokoto.


Cikin sanarwar da ta fitar ta hannun Manjo Hakeem Otiki, rundunar sojin ta ce dakarun nata sun fafata ne da yan bindigar a yankunan Rabbah da Burkusuma a Sokoto, sai kuma Batsari, Safana da Kankara a jihar Katsina, sai dai babu karin bayani kan adadin yan bindigar da aka halaka.

Bayaga tarin makamai, sojin Najeriyar sun kuma yi nasarar kwace Babura akalla 25-daga hannun yan bindigar.

Ko a ranar Juma’ar da ta gabata, dakarun Najeriya sun yi nasarar halaka yan bindiga 15 a yankin Dansadau da ke jihar Zamfara.