rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Zaben Najeriya Muhammadu Buhari

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Buhari ya nada sabbin mataimaka 11

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP/SAUL LOEB

Jim kadan bayan tabbatar Boss Mustapha a matsayin sakataren gwamnatin Najeriya, da kuma Abba Kyari kan mukaminsa na shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya sake nada Karin wasu hadiman fadar gwamnatinsa.


Karin Jami’ai 11 fadar shugaban kasar ta sanar da nadawa a wannan Juma’a.

Daga cikin sabbin jami’an kuma akwai, Ya’u Shehu Darazau, mataimakin shugaban kasakan ayyuka na musamman, Muhammad Sarki Abba, a matsayin mataimakin shugaban kasa kan gudanar da harkokin yau da kullum a fadar gwamnati, sai kuma Dr Suhayb Rafindadi a matsayin likitan shugaban kasa.

Nadin mukaman, ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya suka kosa bisa jiran ganin wadanda za su bayyana a matsayin mukarraban sabuwar gwamnatin kasar da ta yi tazarce, bayan sake lashe zaben shugaban kasa da ta yi, a watan Fabarairu na 2019 da muke ciki.

Sanarwar kakakin shugaban Najeriyar malam Garba Shehu, ta ce nadin mukaman ya soma aiki ne, daga ranar 29 ga watan Mayu da ya gabata.