Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Zaman kotun sauraron kararrakin zabe ya fuskanci tsaiko

Zaman kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasar Najeriya ya fuskanci tsaiko a wannan Juma’a, bayan da lauyoyin jam’iyyar PDP da na dan takararta Atiku Abubakar suka ce harin ‘yan bindiga ya ritsa da wasu shaidun da suke shirin gabatarwa gaban kotun don kalubalantar sakamkon zaben 23 ga watan Fabariaru na 2019.

Dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar.
Dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar. AFP/ Luis Tato
Talla

Daya daga cikin lauyoyin masu gabatar da karar Chris Uche SAN, yace sun gayyaci shaidu 8 ne a wannan Juma’a domin bada bayani kan abinda suka sani na zargin tafka magudi a zaben shugabancin kasar da ya gabata.

Lauyan ya ce a lokacin da lamarin ya auku, shaidun nasu na kan hanyar zuwa Abuja ne daga jiharZamfara.

Ana sa ran cewa kotun sauraron kararrakin zaben shugabancin na Najeriya karkashin jagorancin mai shari’a Muhammed Garba za ta ci gaba da zama a makon gobe, lokacin da shaidun da PDP ke gabatarwa za su cika 36, kamar yadda lauyoyin masu kara suka nema.

A nasu bangaren lauyoyin masu kare wadanda ake kara sun bukaci kotun ta yi watsi da bukatar lauyoyin PDP da dan takararta na dage zaman zuwa mako mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.