rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Najeriya Kwallon Kafa Gasar Cin Kofin Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ighalo ka iya lashe kyautar takalmin zinare a gasar AFCON

media
Dan wasan Najeriya Odion Ighalo. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany

Dan wasan Najeriya Odion Ighalo ka iya lashe kyautar takalmin zinare, bayan jefa jimillar kwallaye 4 a gasar cin kofin kasashen Afrika ta bana.


A halin yanzu wasanni 2 kawai suka rage a kammala gasar, inda Ighalo ke da kwallaye 4, cike da fatan sake zura kwallo a wasan neman gurbin na uku daza su fafata da Tunisia.

Sauran yan wasan da ke biyedaadadin yawan kwallaye uku da suka ci, sun hada da Sadio Mane na Senegal, Bakambu na Jamhuriyar Congo, Ounas da kuma takwaransa Maharez 'yan Algeria.