rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Gasar Cin Kofin Afrika Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ba zamu sallami Rohr daga aikinsa ba - Pinnick

media
Mai horas da tawagar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles, Gernot Rohr. REUTERS/Heinz-Peter Bader

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, Amaju Pinnick ya ce mai horas da tawagar kwallon kafar kasar Gernot Rohr zai ci gaba da zama kan mukaminsa.


A halin yanzu, shekara guda ta ragewa yarjejeniyar kocin Bajamushe don ci gaba da aikin horar da ‘yan wasan Najeriya, amma tuni makomar ta dade da zama maudhu’in da masu bibiyar kwallon ke muhuwara akai.

Sai dai kamar yadda jaridar wasanni ta Sports Extra ta rawaito, Pinnick, shugaban hukumar kwallon Najeriya, ya bayyana kwarin giwa kan samun nasarorin Rohr a nan gaba, inda ya ce a maimakon kora, za a tura kocin samun Karin horo daga kungiyar Bayern Munich da ke Jamus.

A baya bayan nan tsohon dan wasan tawagar kwallon kafar Najeriya Super Eagles, Segun Odegbami, ya bukaci Gernot Rohr ya ajiye mukaminsa da zarar an kammala gasar cin kofin Afrika ta Masar kekarbar bakunci.

Odegbami ya bayyana haka ne a lokacin wata ganawa da manema labarai kan wasan neman gurbin na uku don lashe lambar tagulla da a yau Laraba za ta fafata da Tunisia, da kuma kayen na Najeriyar ta sha a hannun Algeria da 2-1 a wasan kusa dana karshe gasar cin kofin Afrika, ranar Lahadi.

Segun Odegbami ne ya ciwa tawagar Super Eagles dukkanin kwallayen da Najeriya ta doke Algeria da 2-0 a wasan karshe na gasar cin kofin Afrika a shekarar 1980.