Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisa ta tabbatar da Alkalin alkalan Najeriya kan mukaminsa

Majalisar dattijan Najeriya ta tabbatar da mai shari’a Muhammad Tanko a matsayin Alkalin alkalan kasar, mukamin da a baya ya rike a matsayin mukaddashi, bayan dakatar da tsohon Alkalin alkalai Walter Onnoghen, saboda tuhumar da ake yi masa kan kin bayyana kadarorin da ya mallaka da kuma boye asusun ajiyarsa, wanda daga bisani yayi murabus.

Sabon Alkalin alkalan Najeriya mai shari'a Muhammad Tanko, a lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke rantsar da shi a matsayin mukaddashin Alkalin alkalan kasar ranar 25 ga watan Janairu, 2019, a Abuja.
Sabon Alkalin alkalan Najeriya mai shari'a Muhammad Tanko, a lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke rantsar da shi a matsayin mukaddashin Alkalin alkalan kasar ranar 25 ga watan Janairu, 2019, a Abuja. Nigeria Presidency/Handout via Reuters
Talla

Shugaban majalisar dattijan Ahmad Lawal ne ya sanar da matakin, bayan shafe awanni kimanin 2 sabon Alkalin alkalan yana amsa tambayoyi daga ‘yan majalisar a wannan laraba.

Manyan batutuwan da Alkalin alkalan Najeriyar ya tattauna akai a zauren majalisar dattijan sun hada da cin gashin kan sashin shari’ar kasar musamman kan kudaden gudanarwa, cin hanci da rashawa tsakanin alkalai da kuma matsalolin gidajen yari da kuma bin tsare-tsaren doka wajen zartasda hukunce-hukunce da suka shafi dauri da sauran hakkokin jama’a.

Tabbatar da mai shari’a Muhammad Tanko kan mukamin nasa, ya biyo bayan amincewa da matakin da majalisar alkalan kasar NJC ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.