rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zamfara Tattalin Arziki Rahotanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Bankin Afrika zai zuba jarin farfado da jihar Zamfara

media
Taswirar Jahar Zamfara a Najeriya RFI hausa

Bankin habaka kasuwanci na kasashen Afrika Afreximbank, ya ce zai zuba jarin kusan Dalar Amurka milyan dubu daya a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya. A karkashin wannan yarjejeniya da bankin ya kulla da gwamnatin Jihar Zamfara, za a yi amfani da wadannan kudade ne domin gina wasu masana’antu, filin sauka da tashin jiragen sama, bunkasa aikin gona da kuma hako ma’adinai. Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton da wakilinmu na Abuja  Muhammad Sani Abubakar ya aiko mana.


Bankin Afrika zai zuba jarin farfado da jihar Zamfara 29/07/2019 Saurare