Isa ga babban shafi
Wasanni

India ta yi barazanar kauracewa wasannin Commonwealth

Kasar India ta yi barzanar kauracewa wasannin motsa jiki na kasashen kungiyar Commonwealth da za a yi a shekarar 2022 a Birmingham, muddin aka soke gasar harbi daga cikin wasannin da aka tanada.

Sanjeev Rajput of India, daya daga cikin masu wakiltar kasar India a gasar harbi yayin wasannin Commonwealth. 14/4/2018.
Sanjeev Rajput of India, daya daga cikin masu wakiltar kasar India a gasar harbi yayin wasannin Commonwealth. 14/4/2018. Reuters/Eddie Safarik/File Photo
Talla

India ce ta zama zakara a gasar harbi ta shekarar bara yayin gasar wasannin na Commonwealth da kasar Australia ta karbi bakunci.

A waccan lokacin a gasar harbin kadai India lashe lambobin yabo 16 ciki harda Zinare 7, yayinda kuma a jimlace ta lashe lambobin yabo 66, abinda ya bata nasarar zama kasa ta uku mafi kwazo yayin gasar.

Sai dai a watan Yuni daya gabata, kwamitin tsara yadda wasannin motsa jikin za su gudana ya bayyana shirin soke gasar harbi, matakin da kasar India ta ce zai haifar mata da nakasu ga nasarorin ta na lashe adadin lambobin yabo masu yawa da kuma daraja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.