Isa ga babban shafi
Najeriya

Kungiyar Shi'a ta yi watsi da hukuncin haramta ta

Kungiyar Yan uwa Musulmi IMN ta mabiya Shi’a a Najeriya, tayi watsi da hukuncin wata kotun kasar da ya haramta ayyukanta, tare da bayyana ta a matsayin kungiyar Yan ta’adda.

Wani sashi na arrangamar da aka yi tsakanin Yan Shi'a da jami'an tsaro a Abuja, yayin zanga-zangar neman sakin shugabansu Shiekh Ibrahim Zakzaky da ke tsare.
Wani sashi na arrangamar da aka yi tsakanin Yan Shi'a da jami'an tsaro a Abuja, yayin zanga-zangar neman sakin shugabansu Shiekh Ibrahim Zakzaky da ke tsare. REUTERS/Abraham Achirga
Talla

Kungiyar ta nesanta kan ta daga ayyukan ta’addanci da kuma ayyuka masu alaka da haka, kamar yadda kotun ta bayyana.

Yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, mai magana da yawun kungiyar ta Yan uwa Muslmi Ibrahim Musa, ya ce suna da masaniya kan hukuncin kotun, sai dai zuwa lokacin da yake Karin bayanin, kungiyar ta Shi’a ba ta cimma matsaya kan martanin da za ta maida ba.

Malam Musa ya kuma jaddada yin watsi da zargin da gwamnati ke musu na aikata ta’addanci, da wasu ayyukan masu alaka da shi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.