rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Maiduguri Hakkin Dan Adam BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rahoton yiwa sojojin Najeriya dubu jana'izar sirri ya bar baya da kura

media
Wasu dakarun sojin Najeriya. REUTERS/Warren Strobel

Tsohon Mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bukaci gwamnati ta kafa kwamitin bincike domin tabbatar da zargin cewar rundunar sojin kasar cikin sirri ta binne sojoji sama da 1,000 da suka mutu lokacin yaki da kungiyar Boko Haram a Maiduguri.


Sanarwar da tsohon mataimakin shugaban kasar ya sanyawa hannu da kansa, kamar yadda kafofin yada labaran Najeriya suka rawaito, ta bukaci kafa babban kwamitin shari’a domin gudanar da binciken, sakamakon rahoton da Jaridar Wall Street Journal ta wallafa.

Sai dai ma’aikatar tsaron Najeriya ta hannun kakakinta Kanal Onyeama Nwachukwu tayi watsi da zargin wanda ta danganta shi da labarin kanzon kurege.

Ma’aikatar tsaron ta ce tana gudanar da jana’izar dukkanin sojojin da ta rasa kamar yadda dokokin Najeriya suka tsara a bayyane ga kowa, dan haka babu gaskiya cikin labarin cewa rundunar sojin kasar na da makabarta ta sirri.

Sai dai jaridar ta Wall Street Journal da ke Amurka, ta jaddada cewa labarin da ta wallafa sahihi ne, inda tace rundunar sojin Najeriya ta binne dakarun dubu ko sama da haka da suka kwanta dama a yaki da Boko Haram cikin sirri ne, yayinda shugaban kasar Muhammadu Buhari yayi shirin kai ziyara jihar Borno a watan Nuwamba.

Jaridar ta Wall Street Journal ta rawaito cewar a lokacin ne aka binne sojojin a wani yanki da ke Maimalari, domin boye batun cewa har yanzu mayakan Boko Haram na a matsayin babbar barzana ga dakarun na Najeriya.