Isa ga babban shafi

Duk wanda ya shiga gangamin RevolutionNow ya zama dan ta'adda -IG

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Muhammadu Adamu ya yi gargadin cewar za su dauki duk wanda ya shiga zanga-zangar juyin-juya halin da kungiyar ‘RevolutionNow’ ta kira a fadin kasar ranar litinin mai zuwa a matsayin ‘dan ta’adda.

Babba Sifeton 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu.
Babba Sifeton 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu. NAN
Talla

Sanarwar da Babban Sufeton ya rabawa manema labarai ta ce zanga zangar na iya jefa kasar cikin yanayin tashin hankali, inda ta bukaci jama’a da su sake tunani akai.

Mawallafin ‘Sahara Reporters’ Omoyele Sowore tare da wasu masu fafutukar kare hakkin jama’a suka kira gangamin a fadin Najeriya, domin nuna rashin amincewa da yadda talauci da rashin tsaro da kuma kuncin rayuwa suka yi wa al’ummar kasar dabaibayi.

Gwamnatin Najeriya ta bukaci jama’a da su kara hakuri saboda kokarin da take na shawo kan matsalolin da suka addabi kasar, amma masu shirya zanga zangar sun bukaci jama’a da su yi watsi da bukatar wajen fitowa domin nuna fushin su akai.

Rahotanni sun ce a daren jiya, jami’an tsaron farin kaya sun kama Sowore a birnin Lagos.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.