rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sojoji sun kashe 'yan sandan Najeriya

media
Wasu dag cikin sojojin Najeriya Pulse.ng

Rundunar 'yan Sandan Najeriya ta zargi sojojin kasar da kashe jami’anta guda 3 da kuma raunana wasu da dama lokacin da suka kamo wani mai garkuwa da mutane akan hanyar Ibi zuwa Jalingo da ke Jihar Taraba.


Kakakin 'yan Sandan kasar Frank Mba ya ce, lamarin ya faru ne lokacin da sojojin suka bude musu wuta duk da gabatar da shaidar da ke nuna cewa, su jami’an 'yan sanda ne da ke gudanar da aikinsu.

Sai dai kakakin sojin Kanar Sagir Musa ya ce, 'yan sandan sun ki tsayawa a wurin binciken da sojoji ke yi, kana su suka fara bude musu wuta kafin mayar da martini.

Kanar Sagir Musa ya ce, bangarorin biyu tattauna kan lamarin, inda suka amince da kafa kwamitin bincike a karkashin Mukaddashin Sufeto Janar domin gano abinda ya faru.