rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Guinea Conakry

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban Guinea zai yi bikin sallah a Daura

media
Shugaban Najeriya Muhmmadu Buhari tare da takwaransa na Guniea Conakry Alpha Conde punch

Shugaban Guinea, Alpha Conde ya isa garin Daura da ke jihar Katsina domin gudanar da bikin sallar layya tare da takwaransa na Najeriya, Muhammadu Buhari.


Da misalin karfe 5:20 na yamma agogon Najeriya ne, Conde ya isa Daura a jirgi mai saukar ungulu,I nda ya samu kyakkyawar tarba daga shugaba Buhari da kuma sarkin Daura, Umar Farouk.

Rahotanni na cewa, shugaban na Guinea zai yi sallar idi tare shugaba Buhari a garin na Daura a gobe Lahadi.

Kazalika ana sa ran bakon na Buhari, ya kalli hawan Durbur da Majalisar Masarautar Daura za ta gudanar, yayinda kuma za a nada masa rawani.