rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kano Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban kasar Guinea ya halarci hawan daushen sallah a Kano

media
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu kan rakumiyayin hawan daushe na babbar sallah,inda ya karbi bakwancin shugaban kasar Guenea Alpha Conde Aminiya|rfi

Masarautar Kano a Najeriya ta shirya kasaitaccen Hawan Daushe tare da halartar shugaban kasar Guinea Conakry Alpha Conde.


Conde wanda ya gudanar da sallar idi a garin Daura, a marecen jiya ya halarci bikin hawan sallar da aka yi a fadar mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi na biyu a Kofar Kudu.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya halarrci bikin karon farko tun bayan takaddama da suka samu da sarki Sunusi na biyu.

A bangare daya jamiā€™an tsaro sun tarwatsa wasu gungun masu adawa da karin sabbin masarautu da gwamnatin jihar ta yi.

Kafin tarwatsa su, suna rera wakokin da ke cewa "sarki daya ne a Kano".