rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Najeriya Kwallon Kafa Morocco

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya ta lashe zinare a Morocco

media
'yar wasar tawagar mata ta Najeriya Asisat Oshoala da na Afirka ta Kudu Bambanani Mbane a wasannin nemancin kofin Afika ta Mata Courtesy of CAF

Tawagwar kwallon kafar Najeriya ta mata 'yan kasa da shekaru 20, ta lashe kyautar Zinare a gasar wasannin motsa jiki ta nahiyar Afrika da ke gudana a Morocco.


Najeriya ta samu nasarar ce bayan doke Kamaru da kwallaye 3-2 a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Da fari dai ‘yan matan na Najeriya da Kamaru sun kammala wasan a 1-1, bayan shafe mintuna 120 suna fafatawa, abinda ya kai ga bugun Fanareti.

Najeriya ta taba lashe kyautar Zinare a fagen kwallon kafar mata yayin wasannin motsa jikin nahiyar Afrika a shekarun 2003 da 2007.