rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan garkuwa sun saki mutane 30 da suka sace a Katsina

media
Cikin wadanda aka sace a cewar wasu rahotanni har da kananan yara REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo

Gwamnatin Jihar Katsina a Tarayyar Najeriya ta yaba da yadda ake samun cigaba a tattaunawer da ta ke da 'yan bindiga masu garkuwa da mutane, bayan da suka amince da sakin mutane 30 daga cikin wadanda su ke tsare da su a yanzu haka.

 


Matakin sakin mutanen 30 na zuwa bayan nasarar da aka fara samu a tattaunawar mahukuntan jihar ta Katsina da ke arewacin Najeriya da 'yan garkuwar wadanda tubabbun cikinsu ke shiga tsakani.

Tuni dai gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya tarbi mutanen 30 wadanda bayanai ke nunawa cewa dukkaninsu ‘yan asalin jihar ne ciki har da wata uwa da 'ya'yanta 2.

Rahotanni dai sun bayyana cewa guda cikin tubabbun ‘yan garkuwar ne ya yiwa mutanen 30 rakiya har fadar gwamnatin jihar ta Katsina yayin da ya bayyana cewa an boye mutanen ne a dajin jihar Zamfara, jihar da ta yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane don kudin fansa a Najeriyar.