rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Zaben Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Atiku ya garzaya kotun koli don kalubalantar nasarar Buhari

media
Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugabancin Najeriya Atiku Abubakar. REUTERS/Nyancho NwaNri

Dan takarar shugaban kasa a zaben watan Fabairun 2019 karkashin inuwar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abukabar, ya daukaka kara a kotun kolin Najeriya domin kalubalantar hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe wadda ta tabbatar da ingancin nasarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben.


Daya daga cikin tawagar Lauyoyin Atiku da PDP, Mike Ozehkome mai mukamin SAN, ya bayyana cewa, sun shigar da hujjoji 66 a kotun kolin, yana mai cewa, sun yi amanna kotun sauraren kararrakin zaben ta tafka kuskure wajen yanke hukuncinta.

Sai dai Mr. Ozehjome bai yi karin bayani ba kan hujjojin 66.

A ranar 11 ga watan Satumba ne, kotun karkashin Mai Shari’a Mohammed Garba, ta yi watsi da zargin da Atiku ya yi na cewa, shugaba Buhari ya gaza, sannan kuma bai cancanta ba.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren rahoto kan wannan batu, in  da bangarorin jam'iyyun APC da PDP suka yi tsokaci.

Atiku ya garzaya kotun koli don kalubalantar nasarar Buhari

Rahoton Michael Kuduson kan garzayawa kotun koli da Atiku ya yi.

26/09/2019 - Daga Michael Kuduson Saurare

Kotun ta yi watsi da zargin ne bayan ta ce, PDP ta gaza gabatar da gamsassun hujjojin tafka magudi a zaben da shugaba Buhari na jam’iyyar APC ya samu nasara.

Kazalika kotun ta bayyana cewa, Atiku da jam’iyyarsa sun gaza gabatar da shaidun da za su tabbatar cewa, Buhari ba shi da cikakkun takardun kammala karatu ballantana ya zama shugaban kasa.