rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Majalisar Dinkin Duniya Birtaniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wasu miyagu na kokarin damfarar Najeriya biliyoyin Dala- Buhari

media
Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari a yayin gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya a Amurka Femi Adeshina/ Facebook

Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa Majalisar Dinkin Duniya cewa, wasu miyagun kungiyoyin kasa da kasa na kokarin damfarar Najeriya biliyoyin kudade na Dala.


Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin da yake gabatar da jawabi a zauren Majalsar wadda ke gudanar da taronta karo na 74 a birnin New York na Amurka.

Buhari ya bayyana yarjejeniyar huldar kasuwanci tsakanin kamfanin P&ID na Ireland da gwamnatin Najeriya a matsayin yunkurin damfarar kasar Dala biliyan 9.6.

Wata kotun Birtaniya ce ta bai wa Najeriya umarnin biyan makuden kudaden ga kamfanin na P&ID bayan wargajewar yarjejeniyar iskar gas da aka kulla tsakanin bangarorin biyu a shekarar 2010.

Kamfanin ya cimma yarjejeniya da gwamnatin Najeriya domin gina matatar iskar gas a jihar Cross River, amma yarjejeniyar ta tabarbare bayan shekaru biyu.

Kamfanin ya maka gwamnatin Najeriya a kotun birnin London kan zargin ta da karya ka’idojin yarjejeniyar.

A karon farko kenan da shugaba Buhari ke tsokaci baiunal jama’a kan wannna batu wanda ya haifar da cece-kuce a ciki da wajen Najeriya.

Buhari wanda shi ne na biyar a jerin shugabannin da suka gabatar da jawabi a taron na Majalisar Dinkin Duniya, ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa, yayin da ya caccaki kafafen sada zumunta saboda yadda ake amfani da su wajen yada miyagun ayyuka da tashe-tashen hankula da labaran karya.