rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Sokoto Katsina Zamfara Nijar Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Matsalar tsaro ta tilastawa 'yan Najeriya dubu 40 tsallakawa Nijar - MDD

media
Wasu 'yan Najeriya da matsalolin tsaro suka tilastawa tserewadaga muhallansu. AFP Photo/Sia Kambou

Majalisar dinkin duniya tace matsalolin tsaro a arewa maso yammacin Najeriya, sakamakon hare-haren ‘yan bindiga sun tilastawa sama da mutane dubu 40 tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar cikin watanni 10 da suka gabata.


Rahoton majalisar dinkin duniyar ya ce a ranar 11 ga watan Satumba kadai,’yan gudun hijira akalla dubu 2 da 500 ne suka tsere zuwa Nijar, sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.

Yayin ganawa da manema labarai, mai jami’in da wakilci majalisar dinkin duniyar wajen wallafa rahoton, Babar Baloch, ya ce Katsina, Zamfara, da Sokoto sune jihohin da matsalar tsaron ta fi kamari cikin watanni 10 da suka gabata.

A makon jiya gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da wani rahoton majalisar dinkin duniya kan matsalolin tsaro a kasar.

Cikin wata sanarwa, kakakin shugaban Najeriya Malam Garba Shehu, ya ce rahoton na wakilyar majalisar dinkin duniya Agnes Callarmard, bai yi adalci ba, wajen fayyace gaskiyar halin da ake ciki kan tsaro a Najeriya ba.

Cikin rahoton, majalisar dinkin duniyar, ta bayyana Najeriya a matsayin kasar dake fama da rikicin cikin gida a sassanta da dama, wadanda ke dada kamari, ko da yake rahoton ya yabawa gwamnati kan nasarorin da ta samu kan Boko Haram.

A bangaren tashe-tashen hankula a sauran sassan kasar, rahoton majalisar dinkin duniyar ya bayyana rashin bibiya, talauci, sauyin yanayi da kuma yaduwar muggan makamai a tsakanin jama’a a matsayin wasu daga cikin matsalolin da ke rura wutar matsalolin tsaro da rikice-rikicen da Najeriya ke fuskanta.

Sauran matsalolin a cewar majalisar dinkin duniya sun hada da, yadda gwamnati ke yin amfani da karfi wajen dankwafe wasu kungiyoyi a Najeriyar da suka hada da ‘yan shi’a, ‘yan Kungiyar IPOB da aka haramta, da kuma al’ummar Ogoni.