rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Za mu dauki mataki kan masu yada kalaman kiyayya- Buhari

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari RFI Hausa

A yayin gabatar da jawabin samun ‘yancin kan Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari ya yi barazanar daukar tsauraran matakai kan ‘yan kasar da ke yada kalaman kiyayya a shafukan sada zumunta.


Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a jawabin da aka watsa kai tsaye da kafar talabijin kan bikin cika shekaru 59 da samun ‘yancin kan kasar daga turawan mulkin mallaka a safiyar wannan Talata.

A cewar shugaban “muna ci gaba da mayar da hankalinmu kan laifukan da ake aikatawa ta yanar gizo da kuma yadda ake yada kalaman nuna kiyayya ta dandalin fasahar zamani da sauran kalaman rarrabuwar kawuna.”

Buhari ya bukaci ‘yan kasar da su kiyaye tare da girmama juna wajen bayyana bacin ransu ko kuma damuwarsu kan shafukan sada zumuntar.

Buhari ya bayyanna kiyayya da zamba a matsayin dabi’un da ke haddasa kyamar juna da kuma wargaza al’umma, yana mai cewa, ya yi amanna ‘yan Najeriya za su zabi tafarkin zaman lafiya da samun ci gaba domin daurewar hadin kan kasar.