rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Najeriya Kaduna

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yan bindiga sun nemi kudin fansar daliban da suka sace

media
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i The Nation

Gwamnatin jihar Kaduna a Najeriya, ta ce tana kan tattaunawa da ‘yan bindigar da suka sace dalibai mata 6 da malamansu 2 daga kwalejin Engravers dake karamar hukumar Chikun.


Yayin Karin bayani kan halin da ake ciki, gwamnan jihar ta Kaduna Malam Nasir El Rufa’I yace an soma tattaunawar ce, bayan da ‘yan bindigar suka bukaci biyansu kudin fansa kafin sakin daliban da kuma malaman nasu.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i kan sace dalibai 6 da malamai 2 05/10/2019 - Daga Aminu Sani Sado Saurare

Duk da cewa Kaduna na daga cikin jihohin Najeriya dake fama da matsalolin tsaro a wasu yankuna, sace daliban da 'yan bindigar suka yi ya zama bakon abu.

Tun bayan sace daliban dai rundunar ‘yan sanda a jihar ta kaddamar da farautar Yan bindigar kamar yadda kakakinta Yakubu Sabo ta tabbatar.