rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2020

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a gaban majalisar tarayyar kasar a birnin Abuja Femi Adeshina/ Facebook

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kudurin kasafin 2020 na Naira Tiriliyan 10.33 ga zaman hadin guiwa da ya kunshi mambobin majalisar tarayyar kasar a wannan Talata.


Shugaban wanda ya halarci zauren majalisar da misalin karfe 2 na rana agogon Najeriya, ya gabatar da kudurin kasafin a gaban sanatoci da mambobin majalisar wakilai.

Shugaban ya bayyana cewa, an ware wa majalisar tarayyar Naira biliyan 125, yayin da aka ware wa bangaren shari’a Naira biliyan 110 a kasafin.

A game da ma’aikatun gwamnati kuwa da sauran hukumomi, shugaban ya bayyana kudaden da aka ware musu kamar haka:

Ma’aikatar Ayyuka da Samar da Gidaje- Naira biliyan 262

Ma’aikatar Sufuri- Naira biliyan 123

Hukumar Kula da Ilimin Bai Daya a Matakin Farko- Naira miliyan 112

Tsaro- Naira biliyan 100

Aikin Gona- Naira biliyan 83

Albarkatun Ruwa- Naira biliyan 82

Ilimi- Naira biliyan 48

Lafiya- Naira biliyan 46

Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabashin Najeriya- Naira biliyan 38

Shirin Tallafin Gwamnati ga Al’umma- Naira biliyan 30

Birnin Tarayya- Naira biliyan 28

Hukumar Bunkasa Yankin Niger Delta- Naira biliyan 24.

A yayin gabatar da jawabinsa, shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Ahmed Lawan ya bukaci ma’aikatun gwamnati da hukumomi da su bayyana a gaban majalisar kafin karshen watan Oktoba domin kare kudaden da aka ware musu.

Mr. Lawan ya bayar da tabbacin amince wa da kudurin kasafin kafin karshen wannan shekarar.