Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan sanda sun ci gaba da kai samame gidajen tsare kangararru

‘Yan sandan Najeriya na ci gaba da kai samame kan cibiyoyin gyaran tarbiya ko na tsare kangararru a sassan kasar, biyo bayan umarnin yin hakan da a makon jiya, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bayar.

Daya daga cikin wadanda aka ceto daga cibiyar horas da kangararru a unguwar rigasa dake jihar Kaduna. 19/10/2019.
Daya daga cikin wadanda aka ceto daga cibiyar horas da kangararru a unguwar rigasa dake jihar Kaduna. 19/10/2019. REUTERS/Stringer
Talla

Tun bayan soma kai samamen dai, ‘yan sandan sun bayyana ceto dalibai ko mutanen da aka tsare a makarantun horas da kangararrun kusan 150.

Cibiyar gayaran halin da bada horon sana’o’i ta dake karkashin malam Niga a unguwar Rigasa a jihar Kaduna, ita ce ta baya bayan nan da jami’an tsaron Najeriyar suka dirarwa, inda gwamnan jihar Malam Nasir El Rufa’i ya jagoranci kai samamen, ranar asabar, 19 ga watan Oktoba, 2019.

Sai dai a wannan karon ba kamar sauran makarantun a Kadunan da kuma garin Daura ba, kwamishiniyar lura da ayyukan jin kai a jihar Hafsat Baba, ta ce daga cikin wadanda ake tsare da su cikin sarka da ceto a baya bayan bayan 147, 22 yammata ne, 125 kuma maza. Zalika wasu daga cikinsu ‘yan kasashen Kamaru ne da kuma Jamhuriyar Nijar.

Kwamishiniyar ta kara da cewa wasu daga cikin daurarrun da aka ceto sun shafe shekaru akalla 8 cikin sarka da mari.

Wata majiya da ta nemi a sakaya ta, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewar, makamanciyar cibiyar tsare kangararrun da ‘yan sanda suka kaiwa samame a Katsina cikin makon jiya, itama na karkashin malam Niga ne da jami’an tsaron suka kame.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.