Isa ga babban shafi

Najeriya zata dage haramcin da tayi kan wasu kungiyoyin agaji

Hukumar kula da ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce Najeriya ta yi alkwarin dage haramcin da ta wa wasu kungiyoyin agaji na kasa – da – kasa da ke aiki a arewa maso gabashin kasar da rikici ya wa dabaibayi.

Wata 'yar Najeriya a sansanin gudun hijira
Wata 'yar Najeriya a sansanin gudun hijira Reinnier KAZE / AFP
Talla

Wannan sanarwar ta fito ne daga shugaban hukmar, Mark Lowcock wanda  yace ya gana da masu ruwa da tsaki da kuma hukumomin tsaron Najeriya game da batun.

A watan Satumba rundunar sojin Najeriya ta rufe ofisoshin kungiyoyin Action Against Hunger (ACF) da Mercy Corps a arewa maso gabashin kasar, lamarin da ya sa ake fargabar cewa matsalar jinkai za ta ta’azzara.

Rundunar sojin Najeriyar dai ta zargi kungiyar ta kasar Faransa, wato ACF da taimaka wa ayyukan ta’addanci, ta wajen samar wa ‘yan ta’adda abinci da magunguna.

Lowcock wanda ya bayyana kwarin gwiwar cewa nan da ‘yan kwanaki hukumomin Najeriya za su dage haramcin da suka wa kungiyoyin agajin, ya ce rikicin baya – bayan nan ya raba fiye da mutane dubu dari da 40 da muhallansu, sannan ya jefa sama da miliyan 3 cikin hadarin rashin abinci sakamakon kasa noma da manoma suka yi.

Rufe ofisoshin wadannan kungiyoyi da sojin Najeriya ta yi, shine mataki na baya – bayan nan da ke nuni da tsamin danganta tsakanin ta da kungiyoyin agaji a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.