rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Yola Muhalli

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ambaliya ta mamaye kauyuka 40 a jihar Adamawa

media
Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wani yanki na garin Lokoja a tarayyar Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde

Rahotanni daga jihar Adamawa a Najeriya sun ce ambaliyar ruwa ta mamaye akalla kauyuka 40, dake cikin kananan hukumomi 5.


Sakataren hukumar bada agajin gaggawa a Adamawan Dakta Muhd Suleiman, ya ce iftila’in ya biyo bayan saukar ruwan sama mai yawa a wasu sassan jihar, har na tsawon kwanaki 3, inda y ace mafi akasarin kauyukan da ambaliyar ta shafa suna gabar kogin Benue.

Dakta Suleiman yace kananan hukumomin da ambaliyar ta shafa sun hada da Girei, Numan, Fufore, Yola ta Kudu da kuma Demsa.

Sakataren hukumar bada agajin gaggawar ya kuma yi gargadin cewa, akwai yiwuwar fuskantar Karin ambaliyar, la’akari da cewar ruwan kogin na Benue na ci gaba da karuwa, lamarin ya haddasa yankewar hanyoyin kaiwa wasu karin kauyukan jihar ta Adamawa.