rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Lagos

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gobara ta tafka barna a kasuwar Balogun dake Legas

media
Yadda gobara ta kone shaguna a kasuwar Balogun dake birnin Legas a Najeriya. PM News/Efunla Ayodele

Mummunar gobarar da ta shi a birnin Legas ta yi sanadin tafka hasarar tarin dukiya ta miliyoyin naira.


Gobarar ta soma tashi ne a wani bene mai hawa 6, layin Oluwole dake kasuwar Balogun yayinda, wata gobarar kuma ta kone shagunan dake bene mai hawa 3, a layin Dosunmu dake kasuwar.

Zuwa lokacin wallafa wannan labarai, babu Karin bayani kan musababbin tashin gobarar har kashi 2, sai dai hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas ta ce sanar da shawo kan gobarar, bayan shafe tsawon lokaci jamiā€™an kwana kwana na gwagwarmaya.