Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta kashe sojojin Najeriya a Borno

Akalla sojojin Najeriya 10 sun rasa rayukansu, yayin da guda tara suka jikkata sakamakon harin kwanton- baunar da mayakan Boko Haram suka kai musu a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Wani bangare na mayakan Boko Haram da Abubakar Shekau ke jagoranta
Wani bangare na mayakan Boko Haram da Abubakar Shekau ke jagoranta AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Majiyar sojin kasar ta bayyana cewa, har yanzu akwai karin sojoji 12 da suka bace biyo bayan farmakin wanda ‘yan ta’addan suka kaddamar a yankin Damboa na jihar Borno.

Majiyar sojin da ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce, mayakan na Bopko Haram sun yi wa sojojin na Najeriya dirar mikiya ne a yayin da suke kan hanyarsu ta komawa sansaninsu da ke Damboa, mai tazarar kilomita 88 daga birnin Maiduguri.

Sojojin dai na gudanar da aikin kakkabe masu tayar da kayar-baya ne a wannan yanki.

Rahotanni sun ce, ‘yan ta’addan sun kona motocin sojin biyar, yayin da suka sace manyan bindigogi 6 masu sarrafa kansu a dauki ba-dadin da bangarorin biyu suka yi na tsawon sa’a guda.

Yakin Boko Haram da aka kwashe fiye da shekaru 10 ana fama da shi, ya yi sanadiyar mutuwar jumullar mutane dubu 35, inda kuma kimanin miliyan 2 suka rasa muhallansu, lamarin da ya sa suka nemi mafaka a kasashe makwabta da suka hadada Nijar da Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.