rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya UNICEF Hakkin Mata Ilimi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya ce kasa ta 2 a duniya inda ake aurar yara mata - UNICEF

media
Wasu kananan yara a sansanin 'yan gudun hijira dake garin Yola a arewa maso gabashin Najeriya. AFP/EMMANUEL AREWA

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce Najeriya ce kasa ta biyu a duniya da ake aurar da yara mata masu karancin shekaru.


Asusun na UNICEF ya ce kididdiga ta nuna cewar, kananan yara mata akalla miliyan 23 aka aurar a kasar, wanda hakan ya kawo karshen ci gaban karatunsu.

Wani rahoto da majalisar dinkin duniya ta fitar a baya bayan nan ya nuna cewar adadin kananan yara mata da aka aurar a duniya ya kai kusan miliyan 650.

Babban jamiā€™in asusun na UNICEF a Najeriya Bhanu Pathak, ya bayyana hakan a garin bauchi, yayin bikin cika shekaru 30 da kafa hukumar kare hakkin kananan yara ta duniya CRC, da ya gudana a jihar Bauchi.

Wani rahoto da majalisar dinkin duniya ta fitar a baya bayan nan ya nuna cewar adadin kananan yara mata da aka aurar a duniya ya kai kusan miliyan 650.

Zalika rahoton ya yi hasashen cewa akwai fargabar aurar da karin wasu kananan yaran miliyan 150, nan da shekara ta 2030.