Isa ga babban shafi
Najeriya

Masoya Annabi ne ke yin Maulidi- Sheik Dahiru Bauchi

Wani bangare na al’ummar Musulmin duniya na gudanar da bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammadu Sallahu Alaihi Wasallam, abin da ya sa aka bai wa ma’aikata hutu a wasu kasashe da suka hada da Najeriya.

Bikin murnar Maulidi a birnin Lahore na Pakistan
Bikin murnar Maulidi a birnin Lahore na Pakistan Reuters
Talla

An haifi Annabi Muhammad a ranar 12 ga watan Rabi Awwal mafi rinjayen kauli, wanda shi ne wata na uku daga cikin jerin watannin Musulunci guda 12.

Malaman tarihin Musulunci sun ce, an yi wa shekarar haihuwar Annabi lakabi da shekarar giwaye saboda yadda Allah ya hallaka rundunar Sarki Abraha al-Ashram na Yemen wadda ta shigo garin Makka da nufin rushe Ka’aba.

Malaman tarihin sun ce, rundunar ta Sarki Abraha ta yi amfani da giwaye da nufin kaddamar da farmaki kan Ka’aba amma Allah ya aiko tsuntsaye dauke da tsakwankwani da suka hallaka daukacin mayakan na Yemen saboda karramawa ga Annabi Muhammadu Sallahu Alihi Wasallam wanda aka haifa a wannan shekarar.

A yayin zanta wa da sashen hausa na RFI, babban malamin addinin Islama a Najeriya, Sheik Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa, watan Rabi’u Awwal ya samu daraja ne saboda a cikinsa ne aka haifi Manzan Allah.

Babban Malamin ya kara da cewa, “masoya Annabi da ke damuwa da shi, su suke yin a Maulidi”.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da muka yi da Sheik Dahiru Usman Bauchi kan Maulidi.

12:46

Masoya Annabi ne ke yin Maulidi- Sheik Dahiru Bauchi

Sai dai wani bangare na Malaman addinin Islama na cewa, Maulidi wani al’amari ne da ya saba da sunnah ko kuma koyarwar Manzan Allah, abin da ya sa suke ganin bai halatta a gudanar da shi ba.

Malaman sun kafa hujjar cewa, Manzan Allah da Sahabbansa ba su yi bikin Maulidi ba saboda haka ba shi da asali a Musulunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.