Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnonin APC sun gaji da shugabancin Oshimhole

Rikicin jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya na dada kamari, inda a baya-bayan nan, Kungiyar Gwamnonin APC ta bukaci Adams Oshiomhole ya sauka daga kujerar shugabancin jam’iyyar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole Duisaf.com
Talla

Wata sanarwa da Darekta Janar na Kungiyar Gwmnonin, Salihu Lukman ya fitar, ta bukaci Oshiomhole da ya gaggauta kiran taron Majalisar Zartaswar Jam’iyyar domin tattauna hanyar samar da mafita dangane da matsalolin da APC ke fama da su ko kuma ya yi murabus saboda gazawarsa wajen tafiyar da al’amurran jam’iyyar.

Kodayake Lukman bai yi karin bayani ba game da yadda Gwamnonin na APC 18 suka gudanar da taro har suka cimma matsayar fitar da wannan sanarwa.

Amma kwararan majiyoyi daga Shalkwatan APC a birnin Abuja da wasu jihohin kasar, sun ce gwamnonin ba su gudanar da wani taro a baya-bayan ba da zummar tattaunawa kan salon shugabancin Oshiomhole ko kuma rikicin da ke addabar jam’iyyar.

Sai dai ana ganin muddin gwamnonin suka ki fitowa karara domin nisanta kansu da wannan sanarwa ta Lukman, hakan na nufin cewa, da yawunsu aka fitar da ita.

Rahotanni sun tabbatar cewa, tun gabanin zaben 2019, kawunan jiga-jigan jam’iyyar APC suka rarraba, inda wasu ke goyon bayan Oshiomhole, wasu kuma ke adawa da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.