Isa ga babban shafi
Najeriya

Dino Melaye na fafatawa da Smart Adeyemi a zaben Kogi ta Gabas

Yayin da a yau ake gudanar da zaben gwamnonin jihohin Bayelsa da Kogi a Najeriya, wani zabe dake daukar hankalin jama’ar kasa baki daya shi ne zaben kujerar dan majalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta gabas, inda ake fafatawa tsakanin Sanata Dino Melaye da Sanata Smart Adeyemi.

Wani jami'in hukumar zaben Najeriya.
Wani jami'in hukumar zaben Najeriya. REUTERS/Adelaja Temilade
Talla

A Zaben da ya gudana a farkon wannan shekara, Sanata Melaye na Jam’iyyar PDP mai rike da kujerar tun shekarar 2015 ya kada Adeyemi na Jam’iyyar APC, amma sai kotun sauraren shari’ar zabe ta soke zaben saboda korafin daJam’iyyar APC tayi na tafka magudi.

Ita kotun daukaka kara ta amince da zargin da APC tayi, inda ta soke zaben ta kuma bada umarnin sake gudanar da wani sabo

Wadannan ‘yan takara biyu, Adeyemi na APC da Melaye na PDP sun dade suna takun saka tsakaninsu, kuma Melaye ya lashe kujerar a shekarar 2015 a karkashin APC, Sanata Smart Adeyemi, wanda tsohon shugaban ‘yan jaridun Najeriya ne ke rike da kujerar a karkashin Jam’iyyar PDP.

Kamar yadda masu sharhi ke fadi, guguwar APC ta taimakawa Melaye kada Adeyemi a shekarar 2015, kafin daga bisani ya bi su sanata Bukola Saraki sauya sheka zuwa PDP, kana shi kuma Sanata Adeyemi ya koma APC.

Kafin soke zaben kujerar Melaye, yayi kokarin samun takarar kujerar gwamna a karkashin PDP amma Injiniya Wada ya kada shi.

Sakamakon wannan zabe zai tabbatar da wanda jama’ar mazabar Kogi ta Gabas suka fi so tsakanin Sanata dino Melaye da Sanata Smart Adeyemi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.